Garban Kauye ya aike da Sakon ta’aziyyar Sarkin Gaya ga Mataimakinsa da al’ummar Masarautar Gaya

Date:

Daga Halima M Abubakar

Shugaban karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban Kauye Farawa ya nuna alhini da juyayi kan rasuwar Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir, Kirmau Mai Gabas, yana mai bayyana shi a matsayin “daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya wanda ya taimaka wajen Kare martaba da kimar masarautar a idon Duniya.

Alhaji Hassan farawa ya bayyana hakan ne Cikin Wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman Kan harkokin yada labarai Shazali Saleh Farawa ya aikowa Kadaura24.

“Da yakl samun labarin Rasuwar ya yi matukar kaduwa, Shugaban ya lura cewa marigayi sarkin mutum ne mai Hakuri wanda ya bauta wa jama’arsa Babu son zuciya cikin sadaukarwa wanda yace za’a Dade Tarihin Kano da masarautar Bai manta Dashi ba, saboda jajircewarsa ga ci gaban yankin koyaushe.”

Farawa ya Aike da sakon Ta’aziyya ga Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Majalisar Masarautar Gaya, Mataimakinsa kuma Ajiyan Gaya Hon Shamsu Abdullahi Sa’id kademi da Iyalan mamacin, Da fatan Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa ya kyautata makwanci.

7 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...