Nigeria Ta Dakatar da Karbar Digiri Daga Kasashen Togo Da Benin

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da tantance shaidar karatun digiri daga jami’o’in Jamhuriyar Benin da na Togo.

Matakin ya zo ne bayan wani rahoton binciken ƙwaƙwaf da jaridar Daily Nigerian ta yi a baya-bayan nan, inda ta ce wani wakilinta da ya ɓad-da-kama ya samu takardar shaidar digiri daga wata jami’a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida kacal.

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta Najeriya, Augustina Obilor-Duru cikin wata sanarwa da ta fitar, na cewa rahoton ya bayyana hanyoyin da wasu ƴan Najeriya ke bi domin samun takardar shaidar karatun digiri da nufin samun damamrmakin aiki da ba su cancanta ba.

Talla

“Ma’aikatar ilimi ta koka da irin wannan ɗabi’a kuma daga ranar 2 ga watan Janairun 2024, ta dakatar da tantance takardun shaidar karatun digiri daga Benin da Togo har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

“Binciken dai zai haɗar da ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya da kuma ƙasashen biyu da ma’aikatun da ke kula da ilimi a ƙasashen da kuma hukumar tsaro ta farin kaya da hukumar kula da shirin matasa ‘yan hidimar ƙasa, NYSC.”

Wakokin Kannywood 5 Da Suka Fi Shahara A 2023

Ma’aikatar ta yi kira ga yan Najeriya su ba da gudunmawa wajen samar da bayanan da za su taimaka wa kwamitin yayin da yake neman hanyoyin magance faruwar haka a gaba.

Ma’aikatar ta kuma yi bayani kan ƙalubalen da take fuskanta game da matsalar bara-gurbin makarantun ƙetare ko a cikin gida waɗanda mutanen da ba su ji ba su gani ba, ke faɗawa tarkonsu ko kuma wasu ƴan Najeriya waɗanda da saninsu suke karatu a makarantun.

Ma’aikatar ilimin ta ce za ta ci gaba da nazari domin toshe duk wata kafa da hanyoyi da tsare-tsare tare da ladabtar da jami’an da ke da hannu a irin wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...