Daga Rahama Umar Kwaru
Tsohon kwamishinan harkokin Noma na jihar Kano Dr. Yusuf Jibril JY ya bayyana cewa tarihin dimokaradiyyar Nigeria ba zai Cika ba , sai an sanya shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, saboda gudunnawar da ya bayar a siyasance .
” Ganduje ya rike mukamai daban-daban a siyasance da kuma lokacin mulkin soji, hakan tasa yake da kwarewa sosai a fanni siyasa da mulki, hakan ce ma tasa yan adawa suka kasa cimmasa kuma kullum yake kara yi musu nisa”.

Dr. Yusuf Jibril JY ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwat taya tsohon gwamnan Kano Ganduje Murnar cikarsa shekaru 74 da haihuwa, wadda ya sanyawa hannu da kansa kuma aka aikowa kadaura24 a Kano.
Shugaban Kasa Tinubi ya Taya Shugaban APC Na Kasa Ganduje Murnar Cika Shekaru 74 da Haihuwa
” Babu shakka duk Dan dimokaradiyya dole ya yi Murnar cikar Ganduje shekaru 74, saboda ya yi amfani da shekarun wajen hidimtawa dimokaradiyya da yan siyasa tare da bada gudunnawa wajen cigaban jihar Kano da Nigeria baki daya”. Inji Dr. JY
“ Dr. Abdullahi Umar Ganduje kwararren dan siyasa ne kuma kwararren ma’aikacin gwamnati wanda ya faro siyasa da aikin gwamnati tun daga tushe har ya Kai ga matakin kololuwa.

“A madadin ni kaina da iyalaina, masoya da magoya bayan jam’iyyar mu ta APC na kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, muna taya jagoranmu Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 74 masu albarka kuma muna fatan Allah ya kara masa lafiya nasara da nisan kwana”. A cewar Hon. Dr. Yusuf Jibril JY.