Daga Hafsat Sheka
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 74 da haihuwa.
Yayin da ya ke yaba wa irin jagoranci na tsohon Gwamnan jihar Kano, Shugaban ya bayyana Dr. Ganduje a matsayin mai cikakken kishin Dimokradiyya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima da kuma Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Rundunar Yan Sanda ta Kano ta Bayyana Sunayen Mutane 72 da Ta ke Nema Ruwa A Jallo
“Ina taya Shugaban jam’iyyar mu ta kasa murnar cika shekaru 74 a yau, Dr. Abdullahi Ganduje dan siyasa ne kuma kwararren ma’aikacin gwamnati wanda ya faro tun daga tushe har zuwa ga kololuwa.
“A mu’amala ta da shi Dr. Ganduje ya nuna cewa shi amini ne na gari, ya sadaukar da komai nasa ga al’umma, bayar da duk abin da ya yi imani da shi, tun da ya zama shugabanmu, jam’iyyar mu take ta samun nasara kuma hakan ya tabbatar da shi a matsayin ƙwararren ɗan siyasa,” in ji Shugaba Tinubi.

Yayin da yake yi wa Dakta Ganduje fatan alheri da kuma koshin lafiya, Shugaba Tinubu ya roki shugaban jam’iyyar APC na kasa da kada ya yi kasa a gwiwa wajen yi wa Nijeriya hidima.