Gawuna ya baiwa ‘yan wasan Kano Dubu Dari ya yin da gwamnatin Kano ta gaza biyan kudaden gudanar da wasannin Guragu

Date:

Daga Ahmad Hamisu Gwale

Gwamnatin Kano ta gaza bayar da kudaden Alawus-Alawus ga tawagar da ke wakiltar jihar a gasar cin kofin masu bukata ta musamman ta kasa.

Gasar masu bukata ta musamman ta kasa ta wannan shekarar, na ci gaba da gudana a birnin tarayya Abuja da kawo yanzu haka kwana biyu ya rage ayi bikin karkare gasar.

An dai tsara gasar zata gudana daga 8 zuwa 14 ga Disambar shekarar da muke ciki a filin wasa na Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja.

Talla

Wakilinmu ya bamu Labarin cewa wasu cikin wakilan ma’aikatar wasanni, da tawagar Yan Jaridu suna ci gaba da shan wahala sakamakon gaza fitar da kudaden Alawus-Alawus din.

Tin a ranar Asabar aka sanarwa tawagar da zasu wakilci Kano a gasar cewa kudaden gudanarwar ta su zai samu jinkiri zuwa ranar Litinin.

Hotunan yadda wata Tirela ta fadi a cikin gadar Hotoro dake Kano

To sai dai a jiya Laraba da aka shiga kwanaki na biyar babu wani yunkuri daga Gwamnatin jihar Kano kan kudaden da ya kamata a saki domin samun damar gudanar da gasar.

Hakan ta sanya yan Jaridu da Wakilan ma’aikatar wasanni da kansu suke ciyar da kansu, bayaga yadda suke fuskantar barazana abubuwan yau da kullum domin su gudanar da rayuwarsu.

Wani da ya bukaci a sakaye sunansa ya ce hatta Kundin da Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya sanya hannu domin amincewa da sakin kudaden gudanarwar na tawagar ya bata, batare da sanin ina ya shiga ba.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya nada wakilai a kananan hukumomi 44

Babu wani yunkuri da aka samu daga Gwamnatin jihar Kano kawo wannan lokaci, domin kawowa tawagar dauki bayan da ya rage Kwanaki a karkare gasar ta wannan shekarar.

To amma Shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano Alhali Bala Ya ce suna bakin kokarinsu kan wannan batu, yana mai bayar da tabbacin za suyi duk mai yiwa domin tawagar su samu dauki na gaggawa.

A gefe gudama tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna da ya samu wakilcin Kabiru Ali Mazadu ya baiwa wasu yan wasan tawagar kyautar Kudi Naira Dubu Dari (100,000).

Gawuna wanda ya bayar da kyautar kudin jim kadan bayan kammala wasan karshe da yan wasan Kwallon guragu na Kano Pillars da yan wasan Pillars Amputee suka samu nasarar lashe Sarkar Zinare a gasar.

Haka Zalika Shi ma dan kwamitin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Alhaji Naziru Wapa, ya bai wa yan wasan Kano Pillars na Para-Soccer da na Pillars Amputee kyautar Naira Dubu Hamsin (50,000).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...