Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba da gaske take ba wajen yiwa musulmi adalci – Falakin Shinkafi

Date:

Daga Hafsat Yusuf Sulaiman

 

Falakin Shinkafi, Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza yace bai gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna damuwarta da abun da sojoji suka yi na sakin bom akan mutanen dake Maulidi a garin Tudun biri dake karamar hukumar igabi a jihar Kaduna.

” Tunda abun nan ya faru duk abun da gwamnatin tayi da sunan alkawari ta yi shi wanda mu Muna ganin gaskiya ba lallai su iya cika alkawuran ba, tunda da da gaske suke da yanzu a lalubo wadanda sukai abun an Kuma fara hukunta su, ba ayi ta yi mana alkawura ba”.

Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar Kadaura24 ta a Kano.

Talla

Yace ya kamata ya zuwa yanzu an kafa kwamitin bincike ko ma an kamo wadanda suke da hannu akan lamarin domin daukar mataki , Maimakon alkawura da ake ta tayi.

Zargin bata tarbiyya: Sarkin Katsina na shirin korar AGILE daga jihar

” Batun diyya ma ya kamata ya zuwa yanzu ake mun ji ma’aikatar tsaron Nigeria ko ita kanta gwamnatin tarayya ta fitar da kudaden da za’a biya diyyar rayukan wadancan bayin Allah da aka kashe ba tare da laifin komai ba”. A cewar Falakin Shinkafi

“Mu a matsayin mu na yan arewa Musulmi ba zamu saurara ba, har sai mun ga an tabbatar da adalci akan wadancan bayin Allah, ta hanyar hukunta masu hannu a lamarin da kuma biyan diyyar rayukan mutanen da aka kashe babu gaira babu dalili”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...