Wani Magidanci da Iyalan sa sun yi Zanga-Zangar neman adalci ga kisan Masu Maulidi a Kaduna

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon aya

 

Wani Magidanci mai suna Aliyu tsoho Abdullahi mazaunin jihar Kaduna ya gudanar da zanga-zangar lumana tare da shi da ‘ya’yanshi da mai dakinsa, domin neman gwamnati ta dauki matakin hukunta Sojojin da suka sa bom a kan masu Maulidi a garin Tudun biri dake karamar hukumar igabi a jihar kaduna.

” Mun yi zanga-zangar ne mu biyar daga ni sai mai dakina da ‘ya’yana guda uku saboda da mu nunawa gwamnati cewa mun gaji da yadda ake kashe yan arewa babu gaira babu dalili da sunan kuskure Kuma a kasa hukunta wadanda sukai, don haka naje har helkwatar rundunar ƴan sandan jihar Kaduna domin mika koken mu”.

Talla

Da yake zantawa da wakilin kadaura24 a jihar Kaduna, Aliyu tsoho yace ya gamsu da irin tarbar da kwamishinan yan sandan jihar yayi masa , sannan ya bashi tabbacin jami’an tsaro zasu gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wadanda aka samu da laifi a lamarin.

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba da gaske take ba wajen yiwa musulmi adalci – Falakin Shinkafi

Da wakilinmu ya tambaye shi ko wadanne irin bukatu ya gabatarwa yan sanda? , Aliyu tsoho yace sun nemi a bayyana sakamakon binciken da za a yi, a hukunta masu hannu a kisan da neman biyan kuɗin diyyar rayukan wadancan bayin Allah da aka kashe ba tare da wani laifi ba.

” Na fadawa kwamishinan cewa idan har ba’a wadancan abun da na lissafa ba, wanda kuma shi duk mutanen arewa suka bukata to wallahi zan tara mutane mu tare hanyoyi mu Kuma hana duk wani aiki a jihar Kaduna har sai an yi mana abun da muke bukata” . A cewar Aliyu tsoho Abdullahi

Yace ya hana matarsa zuwa aiki sannan ya hana ya’yan su zuwa makaranta, duk don su nunawa duniya damuwarsu kan kisan da aka yiwa sama da mutane 127 wanda ko yan ta’adda basu taba yin irin shi ba. ” Amma abun mamaki jami’an da ya kamata su tsare mutane su kuma suke kashe su , babu shakka wannan abun taikaici ne.

Ga hotunan yadda Zanga-Zangar ta kasance

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...