Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin dakatar da wasu daga cikin asusun gwamnatin jihar Kano a wasu bankunan kasuwanci guda 20 a Najeriya.
Mai shari’a I.E Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a wata kara da masu shaguna a filin idi da kungiyar ‘yan kasuwa suka shigar a kan ruguza shagunansu da gwamnatin Kano tayi, wanda suka bayyana a matsayin haramtaccen matakin da gwamnati ta dauka a watan Yunin 2023.

Kadaura24 ta ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar, Alhaji Awalu sai’du, Ifeanyi Nwobodo, Alhaji Sani Uba, Alhaji Abdullahi A. Idris, da wasu mutane 25 sun kai karar gwamnatin jihar Kano, a matsayin masu bin bashi, har naira biliyan 30.
Umarnin yana kunshe ne a cikin daftarin hukuncin da aka bayar a ranar 28 ga Nuwamba, 2023 kuma aka bai wa manema labarai ranar Larabar nan.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito babbar kotun tarayya dake Kano ta umarci gwamnatin jihar kano da ta biya diyyar Naira Biliyan 30 ga masu shagunan da aka rushe musu a filin idi ba bisa ƙa’ida ba.
Karin bayani na nan tafe…