Hukumar kula da Shari’a a Nigeria ta magantu kan rudani game da hukuncin kotun daukaka kara na kujerar gwamnan Kano 

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim
 Hukumar dake kula da shari’a ta kasa (NJC) ta sha alwashin hukunta jami’an shari’a da suke da alhaki wajen haifar da rudani game da  hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan rikicin zaben gwamnan Kano.
 Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da jami’an NJC suka kai hedkwatar kamfanin Media Trust Limited da ke Abuja ranar Talata, kamar yadda Daily trust ta ruwaito.
 Kadaura24 ta tuna cewa kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar 17 ga Nuwamba, 2023 ta soke zaben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna na jam’iyyar adawa ta APC nasara a matsayin gwamnan jihar kano.
Talla
 Amma a cikin takardar kundin bayanan hukuncin kotun da aka fitar kwanaki hudu bayan yanke hukuncin, kotun daukaka kara a rubuce ta canja bayaninta tare da bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben a karshen takardar.
 Sai dai jami’an hukumar Shari’ar sun ce sun samu koke da yawa kan lamarin inda suka yi alkawarin yin nazari tare da ɗaukar matakin da ya dake ga wadanda aka samu da laifin haddasa rudani kan hukuncin na kano.
 “Ba za a yi gaggawar yarda da koke-koken ba, sai an tantance korafe-korafe da farko, wadanda za su duba, sai su aika zuwa zauren majalisa, sai majalisar ta duba ta kuma kafa kwamiti. Za a kirawo alkali da masu shigar da koken domin bin diddigi,” shugaban tawagar ya shaida wa jaridar.
 Jami’in na NJC ya ce hukumar da ke kula da shari’a za ta binciki cece-kucen da ake yi duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hada da CTC da suka saba wa hukuncin kotun daukaka kara a matsayin batun daukaka kara a kotun koli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...