Gidauniyar Farfesa A. A Gwarzo ta ba da Gudummawar Motoci Biyu da kudinsu ya kai Naira Miliyan 70 ga Jami’ar KUST

Date:

Daga Saifulahi Aliyu Madabo

Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ta bayar da gudunmawar motoci guda biyu da kudin su ya kai Naira miliyan 70 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano dake Wudil (KUST).

Motocin wacce daya tana da kujeru 66 kudinta ya kai Naira miliyan 50, sai kuma motar daukar marasa lafiya da kudin ta ya kai Naira miliyan 20, inda Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda yake shi ne Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) ya jagoranci mika su ga Jami’ar dake Wudil a ranar Talata.

A cewar farfesa Gwarzo wanda kuma shi ne Shugaban Jami’o’i masu zaman kansu na Afirka, ya ce wannan karamcin an yi shi ne domin daukaka matsayin ilimi a ciki da wajen Nijeriya.

Ya yi alkawarin jagorantar yi wa Jami’ar KUST rijistar kasancewa cikin ƙungiyar jami’o’in duniya domin ba ta damar yin gasa tare da sauran takwarorinta a faɗin duniya.

Ya bayyana Shugaban Jami’ar ta KUST, Farfesa Shehu Alhaji Musa a matsayin wanda ya yi nasarar lashe kyautar Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo ta wanda yake bai wa ilimin gaba da Sakandare muhimmanci ta shekarar 2021.

A yayin da yake sanar da wannan kyautar, Farfesa Gwarzo ya ce ya bada kyautar ne bisa lura da irin jajircewa tare da kuma hangen nesa na wanda ya ci kyautar wajen ganin ci gaban Jami’ar KUST, inda ya kara da cewa kyautar tana dauke da zunzurutun kudi har Naira miliyan biyar.

Gwarzo ya yi amfani da wannan dama wajen roƙon jami’o’in Nijeriya da su zama wadanda ake gogaggaya da su a duniya har ya zama ana girmama takardar shaidar kammala Jami’o’insu a fadin duniya.

“Takardar Maradi (Jami’ar MAAUN dake Maradi) an amince da ita a duk duniya kuma gwamnatin Nijar da Majalisar Ilimi ta Amurka sun amince da ita. Wudil na daya daga cikin manyan jami’o’i a Afirka, amma tana da buƙatar a rika yaɗa ta sosai, tare da fadada manufofinta domin ta zarce kan iyakoki “, Farfesa Gwarzo ya jaddada.

Ya shawarci Jami’ar KUST Wudil da ta kafa Sashen koyon harshen Faransanci duba da mahimmancinsa.

A na shi jawabin, Shugaban jami’ar ta Wudil Farfesa Shehu Alhaji Musa ya ce ba zai iya lissafa ayyukan da Shugaban MAAUN ke yi a fannin ilimi a ciki da wajen Afirka ba.

Ya mika godiyarsa ga Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo saboda wannan karamci tare da ba da tabbacin yin amfani da motocin inda ya dace.

10 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...