Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin biyan malaman Jami’a ta ASUU albashinsu da aka riƙe lokacin da suke yajin aiki.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a, ta ce Tinubu ya kuma jingine batun manufar gwamnati ta ba aiki ba biya da gwamnati tayi kan malaman bayan tsunduma yajin aiki da suka yi na tsawon wata takwas daga 14 ga watan Febrairun 2022 zuwa 17 ga Oktoban 2022.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi haka ne domin nuna jin-kai ga malaman.
“A yunƙurinsa na rage matsalolin da ake fuskanta a lokacin aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar nan, tare da amincewa da aiwatar da tsare-tsaren da aka cimma a tattaunawar da aka yi tsakanin ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya, Tinubu ya bayar da umarnin jingine batun ba aiki ba biya, wanda zai bai wa ‘yan ƙungiyar ASUU damar karɓar albashin watanni huɗu daga cikin takwas,” in ji sanarwar.
