Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Hukumar da ke kula da lantarkin Najeriya ta amince da sake duba karin farashin wutar lantarki a kasar nan.
An sanar da hukuncin hukumar ne a cikin wata takarda ga kamfanonin rarraba wutar lantarki.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta umarci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) dake kasar nan da su kara farashin harajin su daga ranar 1 ga Satumba, 2021.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa an tabbatar da ƙarin a cikin takarda daga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko, mai kwanan wata 25 ga Agusta, 2021, mai lamba 023/EKEDP/GMCLR/0025/2021.
Takardar ta bayyana cewa Karin zai karu daga N42.44 zuwa 58.94 ya danganta da ajin su.
Ana sa ran sabon karin aikin zai ci gaba da aiki har zuwa watan Disamba kafin a kara samun karuwa a watan Janairun 2022.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya wacce ke kalubalantar Kudirin na karin kudin wutar lantarki har yanzu ba ta mayar da martani ga sabon hukuncin da Gwamnatin ta dauka.