Yadda Yan Sanda da Gwamnatin Zamfara suka kubutar da Daliban Kwalejin Aikin Gona ta Bakura

Date:

Rundunar’yan sandan jihar Zamfara tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara sun kubutar da dalibai 18 da ma’aikatan kwalejin aikin gona da kimiyyar dabbobi ta jihar Zamfara, Bakura.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shehu Mohammed, yace Kwamishinan’ yan sandan jihar be ya kai Daliban gidan gwamnati, Kuma ya mika su ga Gwamnan jihar Mohammed Bello Matawalle.

CP Ayuba N. Elkana yayin mika wadanda abin ya shafa ga Gwamnan ya yabawa Gwamna bisa goyon baya da kwarin gwiwa da yake baiwa Yan Sanda da sauran Masu Hadin gwiwar da suka taimaka wajen samun nasarar kubutar da wadanda aka sace.

Idan za a iya tunawa a ranar Litinin 16 ga watan Agusta, 2021, wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka mamaye Makarantar suka sace wadanda abin ya rutsa da su zuwa wata maboya da ba a bayyana ba.

Sanarwar tace Tun daga wannan lokacin, rundunar ‘yan sanda a karkashin jagorancin CP Ayuba N. Elkana psc da Hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Zamfara da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da karfafa dabarun bincike da nufin kubutar da wadanda aka sace. .

A nasa bangaren, gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya yabawa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro kan kokarin da aka yi na ganin an sako daliban da ma’aikatan da aka sace ba tare da wani sharadi ba.

Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta dauki tsauraran matakai don duba tare da dakile ayyukan masu aikata laifuka a cikin jihar.

Don haka ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su tabbatar da cikakken bin sabbin matakan da aka fito dasu don Magance aiyukan Yan Bindiga a jihar.

Duk wadanda abin ya rutsa da su, suna samun kulawar likitoci daga bangaren Gwamnati da ‘Yan Sanda kafin a Mika su ga Iyayen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...