RUWASA ta fi kowacce hukuma kazanta cikin shekaru 2 a Kano – Dr Kabiru Getso

Date:

By Sani Magaji Garko

Maaikatar Muhalli ta jihar Kano ta ce bata taba ganin hukuma Mai kazanta cikin shekaru biyu ba kamar hukumar samar da ruwansha a jihar Kano.

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin tsaftar Muhallin ta Kasuwanni da maaikatu da hukumomin Gwamnatin wacce ake gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a nan Kano.

Kwamishinan ya ce maaikatar Muhallin ta Kuma bawa Hukumar waadin kwanaki 3 da su tsaftace muhallansu ko kuma maaikatar ta dauki mataki na gaba.

Dakta Kabiru Getso ya kuma yabawa hukumar kula da gandun daji ta jihar Kano karkashin Sa’idu Gwadabe Gwarzo dangane da yadda suke kula da tsaftar Muhalli inda ya kara da cewa ya umarci daraktan da ke kula da gurbacewar Muhalli da su ziyarci gidan gandun dajin domin bada shawarar yadda zaa yashe Magudanan ruwanta da suka toshe.

Kwamishinan ya kuma ce maaikatar zata duba yadda zaa kammala ginin sabbin bandakunan da ake aikin su yanzu haka a gidan

A jawabinsu daban-daban, shugaban Hukumar Kula da gandun daji na jihar Kano Sa’idu Gwadabe Gwarzo Wanda Amina Muhammad Dankadai ta wakilta da shugaban Hukumar kula da tashoshin motar Kano Line Nasiru Aliko Koki Wanda Rabilu Hamisu Garin-Danga ya wakilta sun bayyana farin cikin su dangane da ziyarar inda suka bada tabbacin dorewar kula da tsaftar Muhallin.

Daga bisani kwamishinan Muhalli ya ja kunnen matuka baburan Adaidaita sahu da Samari da suke fitowa kwallon kafa da su guji karya dokar tsaftar Muhalli inda ya duk Wanda aka kama zaa hukunta shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...