Sama da dalibai 70 na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Neja, masu garkuwa da mutane sun sako su.
Kadaura24 ta ruwaito, an sace Daliban ne daga harabar makarantarsu tun a watan Yuni.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.
Rahotanni sun nuna Daliban Islamiyyar sun kwashe tsawon kwanaki 88 a hannun masu garkuwar .
PRNigeria tana wallafa adadi tun bayan sace daliban a Arewacin Najeriya. Daliban da aka sace na Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri Suma sun kasance a tsare na tsawon kwanaki 70 yayin da sauran daliban da aka sace na wata Makarantar Baptist a Kaduna suka shafe kwanaki 52 a hannun masu garkuwa da mutane.