Zamu tabbatar Jihohi da Kananan hukumomi sun sami kaso mafi tsoka a lokacin canza dokar rabon dukiyar kasa – Na’Allah Kura

Date:

By Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata yi duk mai yuwuwa domin ganin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi sun sami kaso mafi tsoka a lokacin da ake kokarin canza dokokin da ake amfani dasu wajen raba dukiyar kasa.

Kwamishinan Kudi da bunkasa tattalin arziki na jihar Kano Muhammad Shehu Naallah Kura ne ya bayyana hakan a taron gangamin wayar da kan masu ruwa da tsaki na jihohin Nigeria 36 hanyoyin da zaa bi wajen canza dokar raba dukiyar kaya wanda hukumar raba dukiyar kasa ta ke jagoranta taron da ya gudana a nan Kano.

Muhammad Shehu Naallah Kura wanda babban sakataren maaikatar Dakta Lawan Shehu Albdulwahab ya wakilta ya ce gwamnatocin jihohi da na Kananan hukumomi su ne suka fi kusa da alumma, don haka akwai bukatar a canza dokar wacce sojojin da suka mulki kasar nan sukayi tare da sanya mata hanu.

Ya ce idan aka rage kason gwamnatin tarayya aka karawa jihohi da kananan hukumomi hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan tun daga tushe.

“Makasudin shirya wannan taro shine domin wayar da kan masu ruwa da tsaki a shaanin raba dukiyar kasa wanda hukumar raba dukiyar kasa ke shiryawa, akwai tsaruka biyu, daya wanda tarayya da jihohi da kananan hukumomi ke amfani dashi wajen raba dukiya, dayan kuma wanda kananan hukumomi da mazabu kanyi amfani dashi wajen raba dukiyar su” Inji Naallah.

A jawabinsa, sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce gwamnatin jihar Kano zata rubuta takadda ga kungiyar gwamnonin Arewacin kasar nan domin ganin sun yi Magana da murya daya a lokacin da zaa canza dokar raba dukiyar kasa.

Alhaji Usman Alhaji ya ce abin da kowa ya sani ne gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi suke kusa da alumma kuma su ke da kaso mafi karanci a lokacin raba dukiyar kasa, wanda hakan ke bukatar canza dokar.

Ya ce “yakamata a rage kaso 52 cikin 100 da ake bawa gwamnatin tarayya ba kamar yadda ake bawa jihohi kaso 26 cikin 100 ko kaso 20 cikin 100 da ake bawa kananan hukumomi”.

A nasa bangaren, Kwamishina a hukumar raba dukiyar kasa dake wakiltar jihar Kano Barista Umar Faruk Abdullahi ya ce taron ya mayar da hankali kan yadda masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyar masu masanaantu ta kasa reshen jihar Kano da kungiyar cibiyar kasuwanci ciniki da masanaantu da kungiyar Yan Jaridu ta kasa reshen jihar Kano da ma sauran jamaa zasu bayar da raayoyin su domin samar da dokar.

Barista Umar Faruk Abdullahi ya bada tabbacin cewa dukkan raayoyin da aka bayar zasu tabbatar da anyi amfani da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...