Duniyar Aikin Jarida ta yi rashin Isa Abba Adamu tsahon Shugaban BBC Hausa

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa

Allah ya yiwa kwararen Dan Jaridar nan Kuma tsohon Ma’aika’cin Sashin Hausa na BBC Isa Abba Adamu Rasuwa.

Isa Abba Adamu ya rasu ne a Lahadin nan a birnin London na Kasar Birtaniya.

Cikin Wata sanarwa da Dan uwan Mamacin yusha’u Adamu Wanda ya yi aiki Gidan Jaridar Daily Trust yace za a binne Isa Abba Adamu a can birnin Landan, Amma yace “duk da haka, akwai Salatil Gha’ib a gidan danginmu tare dake Lamido Crescent kusa da Express Radio da ƙarfe 9 na safe. Muna bukatar addu’o’in ku”. Inji Yusha’u

Marigayi Isa ya taba zama shugaban Sashin BBC Hausa a shekarar 1990 sannan kuma ya rike Babban Editan na BBC Afrika.

Wasu daga cikin abokan aikin Isa Abba Adamu sun bayyana Mamacin Matsayin Mutum Mai girmamawa da kiyaye lokaci. “Yana cikin gidan Bush kullum da ƙarfe 6 na safe yake gudanar da tarurrukan lokacin da yake shugaban Afirka da Gabas ta Tsakiya Kuma yayi shubanci abin koyi.” Allah ya jikansa da rahama Amin.

Kadaura24 ta rawaito cewa Bashir Gentile gudane cikin Waɗanda Suka mu’amalanci Mamacin ya Kuma bayyana shi a Matsayin Mutum na gari da a koda yaushe yake kula da aikinsa. Ya Kuma ce Rashin sa ba karamin Rashi bane mai girma ga Duniyar Aikin Jarida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...