Daga Nasir Ahmad Zango
Lahadi, 8 ga Agusta, 2021
An sanyawa helkwatar gidan talabijin na farko dake aikin yada labarai Cikin harshen Hausa da ke Kano sunan shahararren Dan Jaridar nan Alhaji Halilu Ahmed Getso don yabawa da irin gudunmawar da ya bayar a aikin jarida a Najeriya.
Shugaban kuma wanda ya samar da tashar, Alhaji Ibrahim Makama ne ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki na tashar dake Kano Wanda aka aikowa Kadaura24.
Ya ce an yanke shawarar sanyawa helkwatar Sunan Halilu Ahmad Getso ne duba da irin gudummawar da ya bayar a aikin jarida cikin shekaru hamsin da suka gabata.
“Sunan Halilu Ahmad Getso sunane da a aikin yada shirye-shirye a duk faɗin yankin Afirka da Turai aka san shi musamman ga masu jin harshen Hausa a duk duniya” in ji shi.
A Jawabinsa Alhaji Halilu Ahmad Getso ya ce ya yi mamakin Samun labarin wannan karamci da nasarar da ba zai taba mantawa da ita rayuwar sa ta aikin jarida ba.
“Ban taba sanin wanda ya kafa Wannan Gidan Talabijin ba, wataƙila ya san ni amma tabbas shawarar da ya yanke na saka sunana a babban ofishin gidan Talabijin din daya samar, hakan tasa ba tuna kyawawar rayuwata da nayi yayin da nake aiki a Rediyon Najeriya da sashin Hausa na BBC. ”
Alhaji Halilu wanda ya gargadi matasan ‘yan jarida da su daina baiwa kuɗi fifiko yayin gudanar da aikin su, ya kuma nuna godiya kan shawarar sanyawa hedikwatar sunan sa.
Kadaura24 ta rawaito Gidan Talabijin naTambarin Hausa a halin yanzu yana gudanar da aikin gwajine daga Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, kuma zasu fara cikakken aiki nan ba da jimawa ba don yada labarai da shirye -shirye cikin harshen Hausa.