Tinubu zai samar da wani Shirin rage talauci a kananan hukumomin Nigeria

Date:

Daga Hafsat Yusuf Sulaiman

 

Ministar Harkokin Agaji da Rage Talauci a Najeriya, Betta Edu, ta ce ma’aikatarta za ta gina cibiyoyiin agaji a dukkan ƙananan hukumomin Najeriya 774.

 

A cewarta, cibiyoyin za su yi aiki ne a matsayin mataki na korar talauci a hankali, kuma za a ajiye kayan abinci ne da aka samar a cikin gida.

Talla

“A ƙarƙashin mulkina, ma’aikatar agaji za ta rage talauci ta hanyar ƙirƙirar ayyukan yi, da tura wa masu ƙaramin ƙarfi kuɗi,” in ji ministar lokacin da take magana a gidan rediyon tarayya ranar Asabar.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Sake Nada Masu Bashi Shawara guda 14

A watan Agusta ne Bola Tinubu ya rantsar da Edu a matsayin minista bayan ta sauka daga muƙamin shugabar mata ta jam’iyyarsu mai mulki ta APC.

Ana ganin ma’aikatar tata za ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da tsare-tsaren gwamnatin na rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin cire tallafin man fetur, wanda ya jawo ninninkawar farashi a faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano,...

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...