Daga Isa Ahmad Getso
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya mai kula da manufofin tattalin arziki Kingsley Obiora.
Wani rahoto da jaridar Peoples Gazette ta fitar ta ce, yanzu Mista Obiora ya shafe kwana hudu a hannun DSS, inda hukumar take yi masa tambayoyi, inda ta ke duba zargin karkatar da kudi a karkashin Godwin Emefiele, hambararren gwamnan babban bankin.

Mista Emefiele, wanda aka fara nada shi gwamnan CBN a watan Yunin 2014, ya kasance a hannun DSS tun ranar 10 ga watan Yunin 2023, kwana guda bayan da shugaba Bola Tinubu ya tsige shi daga mukaminsa.
An yi Garkuwa da Matan Yan Bindiga a Zamfara
Yayin da wasu alkalan Kotunan tarayya biyu ne suka bayar da umarnin a saki Mista Emefiele, amma hukumar DSS na ci gaba da samun wasu dalilai na tsare shi , inda sukan shigar da sabbin tuhume-tuhume domin maye gurbin wadanda aka fara gurfanarwa a gaban kotu.
Wata majiya mai tushe ta ce an kama Mista Obiora ne a matsayin babban shaida kan maigidan sa Emefiele.
Kungiyar kwadago NLC ta sanar da ranar da zata tsunduma yajin aikin gargaɗi
Mista Obiora, wanda aka haifa ranar 6 ga Maris, 1976, ya kasance babban jami’in tsare-tsare a asusun lamuni na duniya, ya kuma shawarci tsohuwar ministar kudi Ngozi Okonjo-Iweala. Ya kuma kasance mai ba Mista Emefiele shawara har zuwa ranar 2 ga Maris, 2020, lokacin da aka tabbatar da shi a matsayinsa na daya daga cikin mataimakan gwamnoni hudu na CBN.
Mista Tinubu, a karshen watan Yuli, ya nada wani Kwamitin bincike na musamman da zai binciki CBN da sauran hukumomin tarayya da ake zargin sun da satar jama’a. Jim Osayande Obazee ya koma bakin aiki a farkon watan Agusta a babban bankin kasar CBN, in ji jami’ai.