Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun ya ce rashin isassun ‘yan sanda, na kawo wa rundunarsu tarnaƙi wajen daƙile aikata laifuka a faɗin ƙasar.
Da yake gabatar muƙala – ga manyan jami’ai masu halartar kwas na 45 a cibiyar tsara manufofi da dabarun shugabanci ta Kuru a jihar Filato – Mista Egbetokun ya ce rundunar na buƙatar ƙarin ‘yan sanda 190,000 domin tabbatar da ayyukanta na tsaron rayuka da dukiyar al’umma a cikin gida.

Ya ce a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta tanadi cewa kamata ya yi ɗan sanda ɗaya ya kula da mutum 460, a Najeriya ɗan sanda ɗaya na kula da mutum 650 ne.
“Don haka rundunar ‘yan sanda na buƙatar ƙarin jami’ai 190,000 domin kai wa ga mizanin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tanada,” in ji shi.
Gwamnatin Kano ta Magantu kan Zargin yanka Tashar Mota ta Rijiyar Zaki
Babban Sufeton ‘yan sandan ya ce idan ‘yan sanda ba su wadaci ƙasa ba, ba za a iya cimma burin manufofin gwamnati ba.
“Don haka, rashin wadatattun jami’ai, zai iya kawo cikas ga tabbatawar manufofin gwamnati,” in ji shi.