Da dumi-dumi: An rufe wani gidan mai a Jigawa bisa laifin tauye lita

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kwamitin kar ta kwana kan harkokin man fetur a jihar Jigawa ta rufe wani gidan mai mai suna IMG da ke Dutse bisa laifin tauye litarsu ga masu mu’amala da su.

 

Shugaban kwamitin, Kanar Muhd ​​Alhassan (rtd) ya ce sun rufe gidan man ne bayan wata ziyarar bazata da suka kai gidan man da ke babban birnin jihar.

Talla

Alhassan ya ce duk da gargadin da aka yi wa gidajen mai, IMG Petroleum su ki gyara mitarsu kuma bai mallaki ma’aunin man ba wanda ake kira da paraffin.

Nijar ta umarci ‘yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga ƙasar

A cewarsa, a kowace lita 10, gidan mai na rage wa abokan cinikin litar lita 1.4, kwatankwacin kusan N900.

Ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar ba za ta nade hannunta ta rika kallon wasu tsirarun mutane su rika aikata munanan dabi’u don cutar al’umma .

Gwamnatin Kano ta Magantu kan Zargin yanka Tashar Mota ta Rijiyar Zaki

DAILY POST ta rahoto cewa rundunar ta yi alkawarin fallasa sunayen gidajen man da aka gano suna tauye litar mai ga abokan mu’amalar su ba.

Shugaban ya bayyana cewa kwamitin zai ci gaba da kai ziyarar gani da ido zuwa gidajen mai da ke fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...