Wata Kungiya ta Nemi Kotu ta Soke Nadin da aka yiwa Ministar al’adu ta Nigeria

Date:

 

Wata ƙungiyar farar-hula da ake kira ‘Incorporated Trustees of Concerned Nigerians’ ta kai sabuwar ministar raya al’adu, Hannatu Musa Musawa Kotu inda ta buƙaci a soke naɗin da aka yi mata.

 

Ƙungiyar ta kare manufofinta kan bukatar hakan, saboda korafe-korafen da suka biyo bayan gane cewa ministar ba ta kammala aikin yi wa ƙasa hidima ba wato NYSC.

Talla

Masu shigar da karar karkashin jagorancin Deji Adeyanju sun buƙaci kotu ta duba kundin tsarin mulkin ƙasa ta fayyace musu idan mutum na iya haɗa aikin hidimar ƙasa ta NYSC da kuma muƙamin minista a lokaci guda.

Gwamnatin Kano ta Magantu kan Zargin yanka Tashar Mota ta Rijiyar Zaki

Sannan sun buƙaci a ci tarar ministar naira miliyan 100 da kuma naira miliyan ɗaya kuɗin ɓata lokaci a kai ta kotu.

Takardun da suka miƙawa kotu mai shafi 13 sun kuma bayyana cewa, Hannatu Musawa ta amsa cewa yanzu take NYSC ɗinta, kuma an tura ta Abuja domin hidimtawa ƙasa.

Korafin nasu na jadadda cewa babu dokar NYSC da ta amince mai hidimatawa ƙasa ya karɓi wani aiki na gwamnati ko muƙamin siyasa.

Ƙungiyar ta ce ya zama wajibi a yi adalci wajen wannan shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...