Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnatin jihar kano ta musanta wani labarin da ake yadawa wanda ke cewa gwamnatin ta yanka filin ajiye motoci na Rijiyar Zaki, a don haka tace labarin karyata ne bashi da tushe ballantana makama.
A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya fitar, ta bayyana cewa wasu marasa kishin Kano ne suke yada jita-jitar domin kawar da hankalin gwamnatin cigaba da yiwa kano Kano saboda da irin nasarorin da ta samu kawo yanzu.

“Gaskiyar magana ita ce, wani yanki na kasuwanci da ba’a amfani da shi kusan shekaru ashirin da suka gabata a kusa da Rijiyar Zaki/Dorayi Babba wanda aka baiwa wasu daidaikun mutane sakamakon yadda aka bada rahoton cewa ya haifar da tashin hankali a yankin wanda ya haifar da karuwar ayyukan aikata laifuka.
Masu amfanar yankin wadanda akasari masu zaman kansu ne su ne suka bukaci a sauya manufar samar da wurin daga wurin kasuwanci zuwa wuraren zama domin gaggauta bunkasar filin da ke kusa da unguwar da ke kan iyaka da Dorayi Babba da Rijiyar Zaki a kan titin Gwarzo a cikin birnin Kano.
Da dumi-dumi: Tinubu ya Magantu kan juyin mulkin kasar Gabon
Har yanzu dai gwamnatin jihar Kano ba ta amince da bukatar mutanenba, kuma filin wurin da ake magana akansa bai hada da tashar mota ta Rijiyar Zaki ba. Gwamnati za ta samar da dukkan bayanai game da shawarar da ta yanke kan bukatar da masu mallakar kadarorin suka shigar don sauya manufar samar da yankin.
An umurci Hukumar Tsare-tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) da ta duba yiwuwar ko akasin haka kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada.
Don haka muna kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani bayani da ya shafi rabon duk wani fili na jama’a ga wani mutum ko kungiya domin gwamnati ta kuduri aniyar kare wuraren taruwar jama’a domin amfanin al’ummarta da mazauna jihar.