YouTube: Kotu ta yankewa wani tsohon malamin makaranta hukuncin kisa

Date:

Daga Hafsat Yusuf Sulaiman

 

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce, kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Saudiyya da aka fi sani da kotun yaki da ta’addanci ta yanke hukuncin kisa ga dan kasar Mohammed Al-Ghamdi sanadiyyar wasu abubuwan da ya wallafa a shafinsa na X da kuma ayyukansa a shafin YouTube, inda aka yi amfani da abubuwan da ya wallafa a matsayin shaida a kansa.

 

Al-Ghamdi, wanda malami ne wanda ya yi ritaya kuma dan shekara 54, an yanke masa hukuncin kisan ne a ranar 10 ga watan Yuli.

Talla

Takardun kotun da Human Rights Watch ta duba sun nuna cewa dalilin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa shi ne bisa kama shi da laifukan da suka shafi sarki ƙasar da kuma yarima mai jiran gado, kuma laifukan sun tsananta ne saboda kasancewar su a dandalin watsa labarai na duniya wanda ke bukatar hukunci mai tsanani.

Gwamnatin Kano ta musanta kin tantance wasu daga cikin ma’

aikatan da Ganduje ya ɗauka

Joy Xia, mai bincike kan al’amuran Saudiyya a kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch, ta bayyana damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin wani sabon mataki mai ban tsoro a Saudiyya inda kotu za ta iya zartar da hukuncin kisa kawai saboda wallafa sako a dandanlin sada zumunta.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Saudiyya dangane da wannan batu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...