Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya amince da nadin mata 131 a mukamai daban-daban na siyasa a jihar.
Kakakin gwamnan, Bologi Ibrahim, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ce 41 daga cikin wadanda aka nada za su yi aiki a matsayin kodineta yayin da sauran 90 za su kasance a matsayin manyan mataimaka na musamman ga gwamnan (SSAs).

Yayin da yake taya wadanda aka nada murna, gwamnan ya yi kira gare su da su jajirce tare da bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar manufofin gwamnatinsa.
Shugaban Mulkin Soji na Nijar ya bayyana lokacin da zasu mika Mulki ga farar hula
Bago ya ce nadin nasu ya zo ne domin cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe na baiwa mata damar ba da gudummawarsu wajen gina jihar ta Neja.