Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce gwamnatinsu da ta hamɓarar da shugaba Mohammed Bazoum, ba za ta wuce shekara uku a kan mulki ba.
Janar ɗin ya bayyana haka ne a jawabinsa ga ‘yan Nijar a kafar talabijin ranar Asabar da yamma.

Shugaban mulkin sojin kuma ya koka da takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasar, yana cewa ta yaya za a hana shigar da magunguna cikin ƙasa a bar mutane na mutuwa a asibitoci?
Abin da Bazoum Ya Fada Mana – Shugaban Tawagar ECOWAS, Abdulsalami
“Ba za a tilasta mu amincewa da abin da ba mu yarda da shi ba,” in ji Tchiani.
Ya ƙara da cewa “waɗannan takunkumai sun saɓa wa aƙida da manufar kafa ƙungiyar ta Ecowas ko CEDEAO na yancin kai-komon jama’a da dukiyoyinsu”.
Muna goyon bayan ECOWAS ta dawo da Mulkin Dimokaradiyya Nijar – yan Nijar mazauna Kano
Shugaban sojin ya ce yana tunanin ƙungiyar Ecowas, ba ta auna illar da harin soji zai haddasa a yankin ba.
Tchiani ya ce ƙungiyar ta manta cewa jajircewar sojojin Nijar ce ta hana yankin Afirka ta Yamma aukawa cikin yanayin rashin tabbas