Sojojin Nijar sun fara daukar yan sa kai don kare kasar daga harin ECOWAS

Date:

 

Daruruwan matasa ne suka taru a birnin Yamai domin ɗaukarsu aikin sa kai a Nijar, a wani yunƙuri na kare ƙasar daga farmakin Ecowas.

Rahotonni na cewa an shirya ɗaukar matasan aikin sa kan ne domin mayar da martani idan ƙungiyar Ecowas ta kai wa ƙasar farmaki.

Ana gudanar da aikin ɗaukar ‘yan sa kan ne a wani ɓoyayyen wuri a Yamai babban birnin ƙasar, to sai dai an hana ‘yan jarida zuwa inda ake aikin ɗaukar ‘yan sa kan.

Muna goyon bayan ECOWAS ta dawo da Mulkin Dimokaradiyya Nijar – yan Nijar mazauna Kano

Ba a dai sani ba ko sojojin da suka yi juyin mulkin na sane da aikin ɗaukar ‘yan sa-kan.

Talla

BBC Hausa ta rawaito Rahotonni da ke fitowa daga ƙasar sun ce, ana sa ran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar-baya a ƙasar za su tallafa wa sojojin da magunguna da kayan aiki sauran dabaru idan Ecowas ta ƙaddamar da yaƙi a ƙasar.

A ƙarshen taron hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas da aka gudanar da Ghana ne aka amince da saka ranar far wa Nijar da yaƙi.

To sai dai ƙungiyar ba ta bayyana takammiyar rana ba, amma ta ce dakarunta a shirye suke domin fara kai farmaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...