Daga Aisha Aliyu Umar
Wani dan jaridar a Kano mai suna Faruk Malami Sharada ya bukaci hukumar tace fina-finai ta jihar da Kuma hukumar Hisbah da su ɗauki matakan da suka dace don hana Sadiya Haruna da Mijinta G-Fresh Al-ameen cigaba da tozarta aure da suke yi a shafukansu na sada zumunta.
” Wadannan mutane guda biyu abubuwan da suke yi ya fara wuce gona da irin don haka akwai bukatar hukumomi irin su Hisbah da hukumar tace fina-finai su ladabtar da su don gudun kar su sa a rika ganin kamar haka Musulmi suke”.

Faruk Malami ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Kano.
Muna goyon bayan ECOWAS ta dawo da Mulkin Dimokaradiyya Nijar – yan Nijar mazauna Kano
Idan har ba’a ladabtar da wadannan mutanen ba, to hakan zai sa wasu ma su sake yin irin abun da suke yi, wanda kuma yin hakan zubar da kimar aure ne da Musulunci baki daya.
Faruk Malami Sharada yace ita ma matashiyar nan ‘yar Tiktok mai suna Murja Ibrahim Kunya ya kamata hukumomin su taka mata burki saboda irin fitsarar da take a shafukan sada zumunta.
ECOWAS ta Sanya Ranar da Zata Fara Yakar Jamhoriyyar Nijar
” Abubuwan da Murja kunya take yi sun sabawa tarbiyya musulmai da kuma ta Malam Bahaushe, kuma Babu shakka idan aka barta ba’a ladabtar da ita ba hakan zai sa wasu su fahimci abun da suke yi ba daidai bane kuma su daina”.
Faruk Malami Sharada yace hukumomin addinin musulunci da gwamnatin jihar kano ta kafa ya kamata su tashi tsaye wajen magance abubuwan da ake yi a shafukan sada zumunta wadanda basu dace da addinin musulunci ba.
Sai dai jaridar Kadaura24 ta samun labarin tuni G-Fresh Al-ameen ya amsa wata gayyata da hukumar Hisbah ta yi masa akan wannan batu na auren G-Fresh da Sadiya Haruna, sai dai har yanzu ba wani cikakken bayani daga hukumar game da abun da suka tattauna da G-Fresh Al-ameen.