Iftila’i: Babban Masallacin Zazzau ya rufta ana sallah

Date:

Daga Aisha Muhammad Adam

 

Ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu a babban Masallacin Zariya da ke ƙofar fada, bayan ruftawar ginin mai tsohon tarihi na Masarautar Zazzau.

 

Wata majiya daga fadar Sarkin Zazzau ta ce ana ci gaba da aikin ceto bayan aukuwar lamarin a Juma’ar nan.

Talla

Rahotanni sun ce rufin wanda na ƙasa ne ya rufta a lokacin da ake gudanar da Sallar La’asar.

 

Babu cikakken bayani a yanzu kan yadda lamarin ya faru.

Yanzu-Yanzu: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya hakura da cikin cikin ministocin Tinubu

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna mutane ɗauke da shebura suna yashe ƙasar da ta rufta a tsakiyar masallacin.

An kuma ga wani da ke nuna yadda rufin ginin a wani sashe na tsakiyar masallacin ya ɓare har ana iya hango sama a lokacin da aikin ceton ke ci gaba da gudana.

BBC ta rawaito Masallacin, tsohon gini ne da aka yi shi cikin fasali irin na gine-ginen Hausawa da yawan ginshiƙai da ke tashi daga jikin ganuwa har zuwa rufin ginin, sannan su tanƙwara su sauka a ɗaya ɓangaren

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...