Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya janye sha’awar sa na kasancewa ciki ministoci kuma dan majalisar zartarwar gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Wasu majiyoyin daga fadar shugaban kasa sun bayyana mana cewa El-rufa’i ya shaidawa Tinubu a wata ganawa da suka yi a ranar talata cewa ba ya sha’awar zama minista, amma zai ci gaba da ba da gudummawar sa domin ci gaban Najeriya a matsayinsa na dan kasa.

Ya kuma shaida wa Tinubu cewa yana bukatar lokaci don mayar da hankali kan kan Karatunsa na samun digirin digir gir a wata jami’a dake kasar Netherlands.”
Rikicin Aure: Ya kamata Hukumar Hisba ta shiga tsakanin G-Fresh da Sadiya Haruna – Auwal Danlarabawa
Majiyar ta shaida wa yan jarida cewa tsohon gwamnan ya ba da shawarar a nada wani makusancin sa a matsayin minista domin maye gurbinsa, mai suna Jafaru Ibrahim Sani, yana mai cewa zai cigaba cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaban kasar don ciyar da ƙasar gaba .
Yanzu-Yanzu: Kotu ta Soke Zaɓen Wani Dan Majalisar Tarayya a Kano
Sani ya taba zama kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kaduna (ilimi da muhalli na kananan hukumomi) yayin da El-Rufai ke gwamna.
Tun bayan ya dawo Najeriya daga Landan, El-Rufai ya nemi ganawa da shugaban kasa, a wannan lokaci ya samu labarin kin tabbatar da shi da majalisar dattawa ta yi.
A ganawarsu, Shugaban kasa Tinubu ya sanar da El-Rufai cewa ya samu korafe-korafe akan sa masu yawan gaske, da yana bukatar rana daya domin ya duba su da kyau sannan ya san wani mataki zai dauka akan su.
A daidai wannan lokaci ne El-Rufai ya shaida wa Tinubu cewa, ya hakura da kujerar ministan, tunda karara na ji a jikina akwai wasu da suka zagaye shugaban Kasa da basa so na zama cikin ministocin sa.