Daga Maryam Ibrahim Muhammad
Shugaban Najeria, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasar da karfe 7 na yamma a ranar Litinin, 31 ga Yuli, 2023.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Litinin.
Shari’ar zaɓen gwamnan kano: Abba Gida-gida ya daukaka kara akan Shaidar APC na 32
Sanarwar ta kara da cewa, “An umurci gidajen talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai da su Kamo gidan Talabijin ta Kasa NTA da Rediyon Najeriya wato FRCN don yada jawabin na shugaban kasar,” in ji sanarwar.