Daga Rahama Umar Kwaru
Hakimin kura Alhaji Tijjani Abubakar Kura, ya hori mawadata da su yi koyi da halin marigayi Alhaji Sani marshall wajen ingantawa da bada gudunmawa ga harkokin Ilimi a karamar hukumar kura da jihar kano baki daya .
” Babu shakka marigayi Alhaji Sani marshall ya taka rawar gani sosai wajen tallafawa al’umma musamman a fannin ilimi, kuma kun san muhimmancin da Ilimi yake da shi a cikin al’umma, saboda haka muke bukatar mawadata su yi koyi da managartan halayen sa don taimakawa al’umma”.

Alhaji Abubakar kura ya bayyana hakan ne yayin bude wani sabon ginin dakin jarabawar da kuma murnar cikar makarantar Sani Marshall Arabic secondary school kura Shekarau 40 da kafuwa.
Hakimin yace tun daga kafa makarantar zuwa yanzu ta yaye dalibai masu tarin yawa, wadanda da yawa daga cikinsu sun zama manyan mutane suna bada gudunmawa wajen cigaban al’umma ta fuskoki da dama.
Matsalar tsaro tasa an Sanya dokar hana fita a Adamawa
A yake nasa jawabin dan marigayin Alhaji Shitu Sani Marshall kura, ya bayyana farin cikinsa sosai bisa yadda aka dade ana amfanar makarantar da mahaifin sa ya gina da kuma yadda ta jima tana yaye dalibai tsahon shekaru 40 da suka gabata.
Yace mahaifin nasu bai rasu ba sai da ya basu tarbiyya, wanda hakan ce tasa suma suke shiga cikin al’amuran da suka shafi jama’a kamar yadda suka ga mahaifinsu yana yi.
ECOWAS ta baiwa sojojin Nijar wa’adin mako guda su mayar da Bazoum matsayin shugaban kasar
” Muna matukar godiya ga gwamnatin jihar kano da ta karamar hukumar kura bisa yadda suke ta bada gudunmawa wajen cigaban makarantar, kuma ina kara jaddada muku cewa zamu cigaba da tallafawa wanann makarantar da ma shiga sha’anin al’umma a kowanne lokaci”. Inji Shitu Sani Marshall
Shitu Sani Marshall yace kafin rasuwar mahaifinsu sai da ya Samar da makarantar a matakan Firamare karamar da babbar sakandire da kuma kwalejin ilimi duk don kishinsa da harkar Ilimi.
Yayin taron wanda aka gudanar da shi a harabar makarantar ya Sami halartar Shugaban karamar hukumar kura da wakilin kwamishinan Ilimi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Ilimi a kura da jihar kano baki ɗaya.