DAGA KAMAL UMAR KURNA
Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin kwashe dukkanin shara tare da tsaftace gidan ajiye namun daji na Kano wato gidan Zoo.
“Wannan ziyara Babu shakka Zara Kara inganta alakar aiki tsakanin hukumarmu ta REMASAB da Gidan zoo, Kuma zamu bada duk gudunmawar da aka bukaci don Kara inganta tsaftar gidan zoo dake waje, don inganta rayuwar al’umma da dabbobin dake gidan”.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan lokacin da shugaban hukumar gudanarwar gidan ajiye namun dajin na Kano Sadik Kura Muhammed ya kai masa ziyara domin neman taimakon hukumar kwashe sharar.
Yanzu-Yanzu: Sojojin Nijar sun Bayyana Sabon Shugaban Kasar
Dan zago yace alhakin hukumar sa ne kwashe shara a fadin birnin Kano matukar an tuntubi hukumar tasa ta hanyar data dace, a dan haka duba da yadda gidan ajiye namun dajin yake da alfanu ta hanyoyi da dama ga al’ummar Kano hukumar sa zata yi abinda ya dace cikin kankanin lokaci.
Da yake nasa jawabin tun da farko shugaban hukumar gudanarwar gidan ajiye namun dajin Sadik Kura Muhammed yace ya je ta REMASAB ne domin neman daukin hukumar, kasancewar dabbobi da al’ummar dake ziyarar gidan na namun dajin suna fuskantar matukar kalubale saboda yadda shara take neman shafe gidan.