Daga Zainab Kabir Kundila
An bayyana Janar Abdurahamane Tchiani a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Nijar, bayan tuntsurar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Sabon shugaban ƙasar ya bayyana a kafar talabijin ta ƙasar, inda ya rinƙa zayyano matsalolin da ya ce ƙasar na fuskanta da suka kai su ga ɗaukan matakin kifar da gwamnatin Bazoum
Daga baya Janar Tchiani ya yi kira ga al’umma ƙasar su bai wa gwamnati haɗin kai ta yadda za a samu nasarar tafiyar da lamurran ƙasar cikin nasara.
A ranar Laraba ne Janar Tchiani ya jagoranci dakaru masu tsaron fadar gwamnatin ƙasar wajen tuntsurar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.
Kuma har yanzu tsohon shugaban na hannun dakarun na Nijar.

Ministoci: Dalilin da yasa Tinubu bai tura sunan kowa daga Kano ba
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a tsakiyar makon nan ne sojojin Kasar ta Nijar suka hambarar da gwamnatin Muhammad Bazoum wanda ya mulki kasar tsahon shekaru 2 da suka gabata.