Daga Aisha Aliyu Umar
Yayin da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya tura sunayen mutane 28 da za a nada a matsayin ministocin kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 ya bukata.
A yau, 27 ga Yuli, 2023, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta jerin sunayen mutane 28 a gaban Majalisar.

Sai dai a yayin da Shugaban Majalisar Dattawa ke karanto sunayen wadanda za’a nada din, har yanzu akwai sunayen da ba fada ba, lamarin da ke nuni da cewa Shugaba Tinubu zai sake tura karin sunayen.
Gidajen siyasar Kano guda biyu wato Kwankwasiyya karkashin jagorancin Jagoran jam’iyyar NNPP ta kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sun shiga rudani na rashin Jin sunan wani daga Kano, wanda shugaban majalisar dattawan ya karata a zauren majalisar.
Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa ta bayyana sunayen wadanda Tinubu zai nada Ministoci
Wata majiya ta shaidawa Majiyar Kadaura24 ta Nigerian tracker cewa dalilin da yasa ba’asa sunan kowanne mutum daga kano ba, shi ne yadda ‘yan jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon Gwamna Ganduje ke matsawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu lamba kan kada ya nada Kwankwaso a majalisar ministoci karkashin gwamnatin APC.
Majiyar ta bayyana cewa sansanin Gandujiyya sun dage cewa sun gwammace su rasa kujerar minista a baiwa babban abokin hamayyarsu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kujerar minista, wanda ya jagoranci faduwar jam’iyyarsu a zaben 2023 a Kano.