Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya magantu kan batun Murabus din da ya yi

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, ya Magantu kan batun murabus din da yayi.

 

Tun bayan da aka samu labarin murabus din nasa a karshen mako, wanda aka kafa jam’iyya mai mulki da shi Abdullahi bai ce komai ba game da lamarin .

 

Amma da aka tuntubi Adamu, ya shaida wa jaridar Daily trust cewa ba zai ce uffan ba a kan lamarin har sai Shugaba Bola Tinubu ya dawo daga taron kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Talla

“Ba zan yi magana game da batun ba saboda shugaban kasa ba ya nan,” Adamu ya shaida wa Daily trust ta wayar tarho.

Tinubu ya bar kasar ne a ranar Asabar din da ta gabata kuma kamar yadda mai magana da yawunsa Dele Alake ya fitar, ya ce shugaban zai dawo kasar ne a karshen taron.

Ku Maida hankali ku koyin aiki don ku taimakawa al’umma -Phrm. Hisham ya fadawa Dalibai

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo gida kowane lokaci daga yanzu.

Wani dan jam’iyyar ta APC ya ce Abdullahi Adamu ya yi murabus ne a lokacin da ya samu labarin cewa wasu manyan mutane guda biyu na kusa da shugaban kasar suna kitsa yadda za’a tsige shi gabanin taron majalisar koli na jam’iyyar da za a yi a ranakun Talata da Laraba.

 

Jam’iyyar ta tsayar da ranakun 10 da 11 ga watan Yuli domin gudanar da tarukan jiga-jigan jam’iyyar na kasa da na NEC domin warware muhimman batutuwan da suka shafe ta da kuma rikicin da ke tsakanin jiga-jigan jam’iyyar.

Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: Gawuna bai taya Abba murnar cin zabe ba – Rabi’u Bichi ya fadawa Kotu

Sai dai kuma daga baya an dage tarukan tare da sauya jadawalin.

“Ya yi murabus ne saboda sun fara hada kai don tsige shi a tarurruka masu zuwa, kuma ya yi murabus ne domin ya ceci kansa daga wulakanci,” in ji babban dan siyasar.

Wata majiya ta ce Adamu ya aika wasikar murabus dinsa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.

“Ya yi murabus. An aika da takardar murabus din da ya sanya wa hannu zuwa fadar Villa. Wasikar an aika wa shugaba Tinubu. Amma tun da shugaban kasar ya tafi Kenya don halartar taron kungiyar AU, an aike da wasikar zuwa ga shugaban ma’aikatansa,” inji majiyar.

Adamu ya kwashe watanni 15 a ofis. A karshen wa’adinsa ne dai ya yi takun-saka da wasu jiga-jigan jam’iyyar kan manyan mukaman majalisar dokokin kasar, wadanda ya ki amincewa da su, amma rahotanni sun ce ya bar maganar ne biyo bayan tsoma bakin Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...