Daga Zubaida Abubakar Ahmad
Gwamnatin da ta shude a jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin NNPP da ta bullo da wani ingantaccen tsari wanda zai rage wa talakawan jihar radadin da suke ciki a maimakon yin katsalandan a shirin gwamnatin tarayya na tallafawa marasa karfi a jihar.
Tsohon kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba, a ranar Lahadin nan, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannun kuma aka aikowa kadaura24.

Muhammad Garba ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga bayanan jamβiyyar NNPP data yi suka ga tsarin da gwamnatin tarayya zata yi wanda kuma daga baya ta janye, bayan da jamaβa suka nuna damawa akan bayanan.
Malam Garba ya ce tuni wasu jihohin suka yi gaba wajen kafa kwamitoci da za su samar da mafita kan halin da al’ummar su suke ciki, wasu kuma kamar jihar Imo sun kai mafi karancin albashi zuwa N40,000 a matsayin wani matakin na saukakawa al’ummar su, amma gwamnatin NNPP a Kano har yanzu ta kasa bai yi wani kokari na hadin gwiwa ba.
Tsohon kwamishinan ya ce: βA shekarar 2017 a lokacin da ake tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago kan batun mafi karancin albashi na N30,000, amma gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta biya N36,000 mafi karancin albashi kuma ta zama gwamnatin jiha ta farko da ta amince da biyan fiye da abun da gwamnatin tarayya ta biya.”
Ya ce rashin fahimtar hakikanin menene mulki ne ya jawo rashin samun daidaito da kuma yin kalaman da basu dace ba daga manyan jamiβan gwamnatin NNPP a jihar Kano.
Malam Garba ya ce irin wannan lamari ya faru ne a lokacin da sakataren gwamnatin jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, ya bayyana dalilin da ya sa aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano, inda ya yi ikirarin cewa samun alamar kurus ne yasa suka rushe ginin .
Malam Garba ya kara da cewa bayan dakatar da biyan albashin maβaikatan gwamnati da aka dakatar da gwamnatin da ta shude ta dauka tare da rage darajar daruruwan malamai, gwamnatin NNPP, duk da alkawarin da ta yi, ta kasa kafa kwamitin da zai binciki lamarin.
Don haka tsohon kwamishinan ya yi kira ga gwamnatin NNPP da ta rika tunkarar harkokin mulki cikin sauki tare da daina furta kalamai da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban jihar.