Da dumi-dumi: Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Hafsoshin tsaron Nigeria

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Majalisar dattijai ta tabbatar da nadin Hafsoshin tsaron Nigeria da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada a kwanakin baya.

 

Majalisar dattawan ta tabbatar da Hafsoshin tsaron ne bayan tantance su a wani zama na sirri da ya dauki sama da sa’a guda.

Talla

Manyan hafsoshin da aka nada sune; Christopher Musa, babban hafsan tsaron kasa; Taoreed Lagbaja, babban hafsan Rundunar sojin kasa ; Emmanuel Ogalla, babban hafsan rundunar sojin ruwa; da Hassan Abubakar, babban hafsan hafsoshin rundunar sojin sama.

Da dumi-dumi: Kotu Ta Dakatar Da Abba Gida-Gida Daga Rushe Gine-Ginen Jikin Badala

A makon da ya gabata ne Tinubu ya rubutawa majalisar dokokin kasar inda ya nemi a tabbatar da hafsoshin tsaron kasar, inda ya gabatar da bukatarsa ​​a sashe na 18 (1) na dokar rundunar sojin kasar. Dokokin CAP A20 na Tarayyar Najeriya, 2004.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...