Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Majalisar dattijai ta tabbatar da nadin Hafsoshin tsaron Nigeria da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada a kwanakin baya.
Majalisar dattawan ta tabbatar da Hafsoshin tsaron ne bayan tantance su a wani zama na sirri da ya dauki sama da sa’a guda.

Manyan hafsoshin da aka nada sune; Christopher Musa, babban hafsan tsaron kasa; Taoreed Lagbaja, babban hafsan Rundunar sojin kasa ; Emmanuel Ogalla, babban hafsan rundunar sojin ruwa; da Hassan Abubakar, babban hafsan hafsoshin rundunar sojin sama.
Da dumi-dumi: Kotu Ta Dakatar Da Abba Gida-Gida Daga Rushe Gine-Ginen Jikin Badala
A makon da ya gabata ne Tinubu ya rubutawa majalisar dokokin kasar inda ya nemi a tabbatar da hafsoshin tsaron kasar, inda ya gabatar da bukatarsa a sashe na 18 (1) na dokar rundunar sojin kasar. Dokokin CAP A20 na Tarayyar Najeriya, 2004.