Daga Aliyu Abdullahi Fagge
Kamfanin raba hasken wutar lantarki dake kula da jihohin Kano Jigawa da Katsina ya bayyana cewa za’a sami katsewar hasken wutar lantarki a jihar kano sakamakon wasu aikace-aikace da zasu gudanar.
” Muna sanar da al’umma cewa zamu sami katsewar hasken wutar lantarki daga yau Asabar zuwa gobe lahadi, sakamakon wani aiki da za’a yi a layin Kaduna/Kano”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar kamfanin KEDCO, wanda ta wallafa a shafin ta na Twitter.
Sanarwar ta tace za’a gudanar da aikin ne domin yiwa wasu injina, sannan sun bada tabbacin hasken wutar zai dawo da zarar an kammala aikin.