Ganduje ya Mika Ta’aziyyarsa ga Iyalai da abokan arzikin MK Alhaji

Date:

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Bayyana Alhinin Sa na Rashin Babban Kwamandan Rundunar Yan Sintiri ta Vigilantee na Jihar Kano Muhammad Kabir Alhaji a yammacin Jiya Lahadi.

Ganduje ya Bayyana Kabir Alhaji a Matsayin Mutumin da yake Jajircewa Wajen Samar da Ingantaccen tsaro a Fadin Jihar Kano baki daya.

Da yake Addu’a yayin Ziyarar Ta’aziyyar da Gwamnan Kano da Mukarraban Sa Suka Halarci Gidan Kwamandan Rundunar Vigilantee na Jihar Kano, Sheikh Ahmad Sulaiman yayi Addu’a Allah ya gafarta Masa.

Da yake Nuna Alhinin Sa na Rashin Babban Kwamandan Vigilantee na Kano, Dr Usman Muhammad Jahun dake Zama Babban Kwamandan Rundunar Vigilantee na Kasa ya Bayyanawa Wakilin Mu Cewar, Lallai Jihar Kano da Tarayyar Najeriya Sunyi Babban Rashin da Baza a taba Manta wa da Shi ba, Musamman da Zarar anji Sunan M K ALHAJI.

A Nasa Bangaren Lamido Alkali dake Zama Qanin Muhammad Kabir Alhaji ya Bayyana Cewar, Lallai Babu Shakka anyi Rashin Mutumin Kirki a Jihar Kano Dama Kasa baki Daya.

209 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...