Daga Auwalu Alhassan Kademi
Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta bayar da tallafi ga karin ‘yan Najeriya da aka dawo da su gida Nigeria sakamakon rikicin Sudan.
Mutum Dari Daya da Ashirin da Biyar (125) na baya-bayan nan da suka hada da nakasassu da dama da Kamfanin Jirgin Sama na Tarco ya yi jigilar su zuwa Abuja a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, kowannensu ya rabauta da Naira 100,000 daga gidauniyar Aliko Dangote.

Idan dai za a iya tunawa, sama da mutane 2,278 da suka dawo gida sun karbi Naira 100,000 kowannensu a watan Mayu, tare da kayan fakitin duk a matsayin tallafi a gare su, da kuma ba su damar haduwa da iyalansu a duk fadin kasar.
Gidauniyar ta sake bada tata gudunmawar ta don samun saukin dawo da ‘yan kasar da aka kwaso daga Sudan kuma daga cikinsu akwai tsofaffi, nakasassu, matasa, mata da yara.
Abba Gida-gida ya bayyana lokacin da za’a fara tura ɗalibai kasashen waje
Wasu mutane biyu ‘yan shekara 70 da suka yi niyyar tafiya tafiya ibadar umrah sun fada cikin rikicin lokacin lokacin da suka ya da zango a Khartoum, Inda kuma kuɗin su ya kara suka rasa duk abun da suka Isa kasar da shi.
‘yan Nigeria da dama ne suka yi asarar sana’o’insu daban-daban sakamakon yakin, sana’o’in da suka hada da fata, dinki, yin takalmi, saye da sayar da dai sauransu
Wani dattijo mai suna Muhammad Saidu Ahmed ya ce, “Na dawo daga Sudan ba ko kwabo ba’, yanzu ina da Naira 100,000

Matar mai shekaru 80, ta ce yawancin iyalanta sun yi nasarar tserewa rikicin, sun shiga tashin hankali sakamakon tashin bama-bamai wanda hakan yasa suka rika fama da yunwa, sannan sun yi asarar gidajensu da wasu daga cikin yan uwansu.
Sun godewa gidauniyar Aliko Dangote, ADF, bisa wannan taimakon, wanda suka bayyana a matsayin wanda ya zo musu basu zata ba, Kuma zai taimaka musu matuka .