Falakin Shinkafi ya Shiryawa Marayu 200 Walimar Sallah a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Falakin Shinkafi Amb. (Dr) Yunusa Yusuf Hamza ya bayyana Sanya farin a zukatan marayu a matsayin wani tushe na neman yardar Allah (S W A).

 

” Mun shirya wannan bikin Sallah ne ga wadannan marayu saboda mu Sanya farin ciki a gare su, kamar yadda iyayen yara suke saka farin ga ‘ya’yansu musamman a wannan lokaci na bukukuwan Sallah babba”.

Tallah

Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata walima da ya shiryawa Marayu akalla dari biyu a unguwar Yakasai dake karamar hukumar birni a kano.

Dr. Yunusa Yusuf Hamza wanda kuma shi ne ya jarman matasan Arewacin Nigeria, ya bukaci sauran al’umma musamman masu hannu da shuni da su rika tunawa da marayu musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

” Kamata yayi yadda muke kula da ‘yan’yan mu , suma wadanda Allah ya karɓi rayuwar iyayensu mu rika kokari ko Yaya mu rika tunawa da su mu kuma rika tallafa musu ko muma Allah ya dube mu ya shiga lamarin mu”. Inji Falakin Shinkafi

A yayin taron walima Dr. Yunusa Yusuf Hamza ya rabawa wasu daga cikin marayun kayan sawa, sanann kuma aka ci abinchin tare da marayu kuma aka dauki hotuna don tunawa da wannan rana ta bikin Sallah.

” Alhamdulillah mun yi farin ciki da wanann rana Kuma ba iya kacin abun da muka shirya musu kenan ba, a gobe Lahadi in Allah ya kaimu zamu kaisu gidan zoo domin dai mu dauke musu kewar rashin mahaifansu”. A cewar Falakin Shinkafi

Talla

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a watanni baya Falakin Shinkafi ya shirya taron zagayowar bikin ranar haihuwarsa a gidan marayu na Nasara a kokarinsa na baiwa marayu kulawar da ta dace.

Marayun sun kasance cikin farin ciki tare da mika godiyarsu ga shi Falakin Shinkafin saboda wannan abun alkhairi da ya jima yana yiwa marayu ba a unguwar Yakasai ba kadai har da jihar kano baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...