Daga Halima Musa Sabaru
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ko kadan baya nadama kan aikin rushewa da kwato dukiyoyin al’umma da gwamnatin da ta shude ta yi na ta mallaka wasu ba bisa ka’ida ba tare da raba wa shanu masu tsarki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero tare da hakimai da sauran ‘yan majalisar Masarautar suka kai wa Gwamnan ziyarar Sallah a gidan gwamnati a wani bangare na bukukuwan Sallah.

“Mai martaba yana da kyau majalisar masarautar kano ta sani cewa mun fara aikin rusau ne domin dawo da kadarorin jama’a da aka mallakawa wasu ba bisa ka’ida ba, kuma za mu tabbatar da cewa an dawo da duk irin wadannan kadarorin domin maslahar mutanen Kano”. Inji Gwamna Abba
Ganduje ya Magantu kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Kano ta yi
Alh. Abba Kabir ya yabawa mai martaba sarkin da ‘yan majalisarsa bisa wannan ziyarar wadda ita ce irinta ta farko tun bayan hawansa mulki a matsayin gwamnan jihar kano.
Gwamnan ya lissafo nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 31 da suka gabata, wadanda suka hadar da; biyan kudin NECO ga daliban makarantun sakandire 55,000 da suka kai naira biliyan 1 da rabi, gyara fitulun tituna da rage matsalar sace-sacen waya a cikin birnin Kano.
Sauran a cewar Gwamnan sun hada da; sake dawo da tantance daliban da za’a basu tallafin karatu zuwa kasashen waje ga ’yan asalin Kano masu digiri na farko, da biyan albashi da fansho da kuma kwashe tarin sharar dake birnin Kano.
A jawabinsa tun da fari Sarkin ya ce sun kai ziyarar ne domin taya Gwamnan murnar bikin Sallah tare da ba da tabbacin cewa a shirye yake ya bayar da shawarwarin da za su kasance masu muhimmanci ga ci gaban jihar, ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran al’umma da su taimaka wa masu karamin karfi wajen ciyar da jihar gaba sakamakon halin da al’umma suka shiga saboda cire tallafin man fetur.