Daga Aisha Aliyu Umar
Majalisar dokokin jihar kano ta ce zata fara tantance sabbin wadanda gwamnan kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya tura musu mata sunayen su a ranar Laraba 21 ga watan Yuni 2023.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnan Abba Kabir Yusuf ya tura sunayen mutane 19 wadanda ya buƙaci majalisar ta tantance su domin ya nada su a matsayin kwamishinoninsa.
Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya tura sunayen wadanda zai nada a matsayin kwamishinoni
Shugaban majalisar Hon. Jibril Falgore ne dai ya karata wasikar da gwamnan ya turawa Majalisar Mai dauke da sunayen.

Da suke bada gudunmawa yayin zaman majalisar na wannan rana, dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado/ Tofa, Muhammad Bello Butu-Butu da na karamar hukumar Ungoggo Aminu Sa’adu Ungoggo, sun bayyana cewa tantance sabbin kwamishinonin da wurin zai taimaka ciyar da jihar kano gaba.
Suka ce tantancewa da Amincewa da sunayen da akan lokaci zai baiwa ɓangaren zartarwa damar rantsar da su akan kari domin fara aikin su don ciyar da jihar kano gaba ta konne ɓangare.
Kwamishinoni sune yan majalisar zartarwa Kuma suna bada gudunmawa ga ɓangaren zartarwa wajen aiwatar da manufofi da kudirorin gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulki Nigeria ya tanada.