Ba za mu amince da ƙaƙabawa majalisa ta 10 shugabanni ba- Zaɓaɓɓun Sanatoci

Date:

Daga Nura Abubakar

 

Wasu zababbun Sanatoci sun sha alwashin yin Allah-wadai da duk wani yunkurin da wasu ke yi na kakabawa majalisa ta 10 shugabannin majalisar wadanda za’a zaba a ranar 13 ga Yuni, 2023 .

Da yake magana a madadin ‘ya’yan kungiyar, zababben Sanata, Suleiman A. Kawu Sumaila, yace yunkurin kakabawa majalisar shugabanni ya saba wa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki da Dokokin Majalisun biyu.

“A ganina, kokarin kakabawa ‘yan majalisar shugabannin, ba kundin tsarin mulki Nigeria kadai ya sabawa ba, ya kuma sabawa dokokin majalisar dattawa da ta wakilai, kuma hakan zai haifar da mummunar rashin fahimta tsakanin ‘yan majalisar da ɓangaren zartarwa ta gwamnati.

Hotuna: Yadda Gwamnatin Kano ta rushe shagunan da aka yi a filin idi

“Rahotannin da muka samu sun nuna cewa wasu ‘yan siyasa wadanda basa kishi dimokaradiyya na shirin yin amfani da hanyoyin da basu dace ba wajen dorawa ‘yan majalisar shugabannin da za su jagorancesu, wannan mataki bai dace da dimokradiyya ba, ba za mu amince da shi ba, kuma barazana ce ga dimokuradiyyar mu da ma kasar baki daya,” in ji shi.

Sumaila ya bayyana cewa, zaben shugabannin al’amurin cikin gida ne da ya shafi ‘yan majalisar kawai, don haka ya kamata a bar su su zabi wanda zasu shugabance su don gudun maimaita abun da ya faru da majalisa ta 7 da ta 8.

Ya kara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya da na majalisar dattawa sun fito karara kan yadda za a zabi shugaban majalisar da mataimakinsa.

“Misali, babi na 2 sashi na 9 na dokokin na Majalisar Dattawa ta 2022 (da aka gyara) ya bayyana hanyoyin zaben shugabannin Majalisar. Hakazalika, sashe na 50 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yiwa gyara) ya bayyana cewa, “za a samar da shugaba da mataimakin shugaban majalisar dattawa, wadanda ‘yan majalisar za su zaba a tsakanin su.
Kuma, Sashe na 50(1)b ya tanadi cewa, “Shugaban majalisa da mataimakinsa, wadanda ‘yan majalisar za su zaba daga tsakanin su ne kadai.

“A halin da ake ciki, ina son in yaba wa shugaban kasa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, GCFR, bisa nada Sanata George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, da kuma nada kakakin majalisar wakilai. Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.

 

“Wannan shi ne karon farko a tarihin dimokuradiyyar mu idan muka samu shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da mataimakin shugaban ma’aikata duk suna da gogewar majalisar. Don haka, yan Nigeria zasu tsammaci mutunta dokokin Tsarin Mulki daga gare su.

“Saboda haka, ina so in yi amfani da wannan damar domin jawo hankalin mai girma shugaban kasa kan wannan yunkurin na cin zarafin dimokuradiyya da wasu abubuwa ake shirin yi da basu da cewa”.

“Hakazalika, ina so in yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki, kungiyoyin farar hula da sauran kungiyoyin duniya da su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da dunkulewar dimokuradiyya a Najeriya.
“Mu ‘yan majalisar da ke goyon bayan takarar Sanata Abdulaziz Abubakar Yari a shirye muke mu yi aiki tare da mai girma shugaban kasa domin samar da ingantacciyar Najeriya.

“Ina da yakinin cewa mai girma shugaban kasa a matsayinsa na dan dimokradiyya na gaskiya wanda ya yi imani da bin doka da oda zai yi duk mai yiwuwa don kare martabar Majalisar Dokoki ta kasa. Mu ‘yan majalisar da ke goyon bayan takarar Sanata Abdulaziz Abubakar Yari a shirye muke mu yi aiki da maigirma shugaban kasa domin samar da ingantacciyar Nijeriya,” ya karkare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...