Daga Isa Ahmad Getso
Tsohon gwamnan jihar kano kuma Sanatan kano ta tsaki Malam Ibrahim Shekarau ya baiwa sabon gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf shawara kan matakan da gwamnatinsa ta fara dauka.
” Yana da kyau ka tsaya ka yi nazari da tare da tuntubar masana akan duk wani hukunci da zaka yanke, saboda yin hakan shi zai hanaka yin dana sani a mulkin ka ,kuma hakan zai taimaka maka wajen samun nasara gudanar da mulkin Kano”.
KAYYASA: Kalli yadda Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya fara rushe gine-gine (hotuna)
Kadaura24 ta rawaito Malam Ibrahim Shekarau ya baiwa gwamnan shawarar ne yayin wata ganawa da sukai da Premier Radio dake kano
” Ka guji yanke wani hukunci don ka farantawa wani ko dan ka bakantawa wani yin hakan ba adalci bane, kuma a matsayin ka na shugaba dole ne ka yiwa kowa adalci, ba laifi ba ne don ka binciki wani abun da baka gane ba , amma yin gaggawar ba ya haifar da alkhairi kamar yadda Annabi S A W ya faɗa cewa ita gaggawa daga shaidan take”. Inji Shekarau
Sanatan wanda shi ne Sardaunan kano ya kuma Kara da cewa baiwa mata Shugaban ya rika yin gaggawa wajen yanke hukuncin ba, idan ya kafa hujja da wani hadisin Annabi (S A W) dake cewa “idan Shugaba ya yanke hukunci da niyyar yin adalci Ida yayi dai-dai to Allah zai bashi lada biyu, idan kuma ya yi kuskure to Allah zai ba shi lada daya” kaga kenan babu asara a jinkirtawar da za’a yi .
Ana ganin dai wannan sharar da Shekarau ya baiwa gwamnan kano tana da nasaba da matakan da gwamnatin Abba Gida-gida take dauka musamman akan wadanda sukai gini ba bisa ƙa’ida ba.