Janye tallafin mai: Ƙungiyar ‘Yan jarida a Najeriya za ta fara yajin aiki

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ ta ce za ta bi sahun ƙungiyar Kwadago wajen tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa, saboda cire tallafin man fertur a Nigeria.

KAYYASA: Kalli yadda Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya fara rushe gine-gine (hotuna)

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ta fitar, bayan ganawar da kwamtin gudanarwarta ya yi da safiyar ranar Asabar domin tattauna batun cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi da kuma matakin ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ɗauka na shiga yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

Ƙungiyar ta NUJ ta ce a halin da ake ciki tashin farashin man fetur da na sauran kayayyaki sun jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ƙungiyar ta umarci mambobinta da ke faɗin jihohin ƙasar da su fara yajin aiki tare da fita zanga-zanga daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni matuƙar kamfanin mai na ƙasar NNPCL bai janye ƙarin farashin man fetur da ya yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...