Wasu ‘yan siyasa na shirin guduwa kafin 29 ga watan Mayu – EFCC

Date:

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ce wasu ‘yan siyasa da take zargi da rashawa na ƙoƙarin ficewa daga ƙasar kafin su sauka daga mulki ranar 29 ga watan Mayu.

Hukumar EFCC ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga Gwamnan Zamfara Bello Matawalle game da zargin da ya yi wa shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa cewa ya nemi rashawar dala miliyan biyu a hannunsa – kwatankwacin naira miliyan 922.

“Idan har Matawalle da gaske yake, ya kamata ya daina ɓaɓatu ya gabatar da hujja ƙarara kan zargin da yake yi,” in ji wata sanarwa da EFCC ta wallafa ranar Juma’a.

Ta ƙara da cewa: “Kazalika, hukumar na ankarar da al’umma cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa da ke shirin ficewa daga Najeriya kafin ranar 29 ga watan Mayu.”

EFCC ta ce Gwamna Matawalle ya fara gabatar da zarge-zargen ne bayan ta ƙaddamar da bincike kan zargin almundahanar naira biliyan 70 a kansa na wasu ayyukan da ta ce an bayar amma ‘yan kwangilar ba su yi ba.

Bello Matawalle na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar na cikin gwamnonin da za su sauka daga mulki a ranar 29 ga Mayu bayan ya sha kaye a hannun Dauda Lawal na PDP a zaɓen watan Maris da ya gabata

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...